Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce, ta kashe dan ta’adda guda daya, ta kwato bindiga kirar AK-47 daya da babura guda hudu da maharan ke amfani da su wajen kai hari a unguwar Mararabar Yakawada da ke karamar hukumar Sabuwa a jihar Katsina.
A cewar mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Katsina SP Gambo Isah, “’yan ta’addan da ba su wuce 30 ba, a kan babura sun tare hanyar Sabuwa zuwa Mararabar Yakawada da nufin yin fashi da garkuwa da mutane.
“Da samun rahoton, jami’in ’yan sanda na sashen Sabuwa, ya jagoranci rundunarsa ta dabara zuwa yankin inda suka yi artabu da ‘yan bindigar, inda suka dakile shirin kai harin na maharan.
“A yayin da ake duba wurin, an gano gawar daya daga cikin ‘yan ta’addan da aka kashe, an kuma kwato bindiga kirar AK-47 daya da kuma babura guda hudu daga wurin.”
A cewar Gambo, yawancin ‘yan ta’addan ana fargabar an kashe su ko kuma sun tsere da raunukan harbin bindiga.