Bayan da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka yi awon gaba da wasu mutane biyu, cikinsu har da wani dan kasar Turkiyya, Erdogan Guler, mai shekaru 52, rundunar ‘yan sandan da ke yaki da masu garkuwa da mutane a babban birnin tarayya Abuja, ta fara gudanar da bincike wajen ceto su.
Wani babban jami’in ‘yan sanda ya shaidawa Vanguard cewa an tura jami’ansu zuwa Kubwa domin yin aiki tare da ‘yan sanda a karkashin rundunar Yansandan yankin.
Majiyoyi sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun bi sawun dan kasar Turkiyya da kuma wani mutum daya da ke tare da dan kasar Turkiyya zuwa wani katafaren gida da ke Kubwa, kusa da babbar hanyar Express inda suka yi awon gaba da su da bindiga da misalin karfe 7 na dare.
Daga baya an kai rahoto ga ‘yan sanda da ke ofishin ‘yan sanda na Dibishin Byazhin Abuja.
Wata majiya ta ce wasu ‘yan bindiga uku da ba a san ko su waye ba a cikin wata mota kirar Toyota Prado SUV, sun yi garkuwa da dan kasar Turkiyya da kuma wanda ke tare da shi a harabar sa (Guler) da ke Leaner Estate, Brickcity, Kubwa.”
Babban jami’in ya yi nuni da cewa, ba wai kawai kokarin kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su ba ne, har ma don bankado wadanda ke da hannu a wannan aika-aika da kuma kama su.