fidelitybank

‘Yan sanda sun fara farautar wanda ya kashe ‘yar shekara 12 yayin fyade

Date:

Yanzu haka rundunar ‘yan sandan jihar Ogun na neman wani mutum da ya yi wa wata yarinya ƴar shekara 12 fyaɗe har yayi sanadin mutuwarta.

Mercy Orija, wanda tsohon mai laifi ne da aka hukunta ya tsare jim kadan bayan da aka baza komar farautarsa.

Babban jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abimbola Oyeyemi ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin.

Yace wanda ake zargin dai tsohon mai laifi ne wanda aka sake shi daga gidan yari.

Ya kara da cewa ‘yan sanda sun kaddamar da farautar mutumin bisa laifin da ake zargi ya aikata.

Mercy Orija, wanda aka samu da laifin cin zarafin wata ma’aikaciyar kudi ta POS a shekarar da ta gabata, kana a yanzu aka sake zarginsa da aikata laifin yiwa karamar yarinya fyade, jim kadan bayan an sako shi daga gidan yarin.

Marigayiyar dai dalibar makarantar sakandare ta sojoji da ke Alamala a Abeokuta.

Rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargin ya ja Janet zuwa cikin wani gida yayin da take komawa gida daga inda ta je siyan sabulu don wanke kayan makarantar ta ranar Laraba.

Ana zargin Orija cewa ya jefar da gawarta a wani gini da ke kusa da gidan ‘yan uwansa kana ya tsere daga wurin.

Wannan abu da ya faru ya harzuka matasan yankin da yayi sanadin suka ƙona gidan dangin wanda ake zargin an aikata wannan ta’asa a ciki.

Mahaifin marigayiyar Sanjo ya ce, “Lokacin da Janet ta zo daga makaranta ranar Laraba, tana aiki a gida kan wani rubutu da aka bata tayi, kuma bayan ta gama, sai ta gaya masa cewa tana son sayen sabulu a gidan maƙwabciyarsu don ta wanke safarta.

Mahaifin yarinyar ya kai rahoto ofishin ‘yan sanda bayan sun neme ta amma basu same ta ba.

A lokacin da suke dawowa daga ofishin ‘yan sanda suka ga cincirindon mutane na cewa sun gano gawar ‘yarsa.”

Mista Fakeye ya ce ya tarar da gawar ‘yarsa a wani gida da ba a kammala ba da sabulun da ta saya da kuma alamun ɗigon wani abu jaja a jikinta.

Kawo yanzu dai ba a kai ga kama shi ba, to amma matasan yankin sun sha alwashin zakulo shi da kuma damƙa shi hannun ‘yan sanda domin ya fuskancin hukunci gwargwadon laifin da ake zarginsa da aikatawa.

daily post

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp