Rundunar ‘yan sandan Jihar Ondo, ta ce tana bincike kan rahoton satar wasu yara a yankin Valentino na jihar.
Rundunar ta faɗa wa BBC Pidgin ranar Asabar cewa, matakin ya biyo bayan labarin da suka samu ne game da wani yunƙuri na sace yaran a loƙaci guda a yankin.
Wani bidiyo da aka yaɗa a dandalin Twitter ya nuna yadda wasu mazauna yankin suka yi wa ofishin ‘yan sanda tsinke don neman ƙarin bayani game da lamarin.
Kakakin ‘yan sandan jihar, Funmilayo Odunlami, ya ce suna kan bincike kuma ya yi kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu.
Jihar Kano ma da ke arewacin ƙasar ta daɗe tana fama da sace-sacen yara, abin da ya sa gwamnatin jihar ta kafa wani kwamati na musamman don ganowa da kuma mayar da yaran da aka sace gida bayan kai su wasu yankuna da kuma sauya musu sunaye a Najeriya