fidelitybank

‘Yan Sanda sun damke ‘yan IPOB a Imo

Date:

Rundunar ‘yan sanda a jihar Imo, ta kama wadanda ake zargin ‘yan haramtacciyar kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra ta IPOB su tara.

Ana zargin mutanen ne da kashe ‘yan sanda biyar da kuma karin wasu mutane a jihar.

A wata sanarwar da kakakin rundunar Henry Okoye ya fitar, ‘yan sandan sun ce sun kama daya daga cikin jagororin mutanen mai shekara 48 ne a maboyarsa a Umuahia babban birnin jihar ta Abia.

Okoye ya ce kwamishinan rundunar ce ya bayar da umarnin kama mutumin domin ya bayyana sauran wadanda suka aikata kisan.

Sanarwar ta kara da cewa mutumin da ake zargin ya tabbatar wa ‘yan sanda cewa shi ne kwamandan ‘yan IPOB a yankin Mbaise a jihar.

Sauran mutane uku da aka kama din duk ‘yan yankin Mbaise ne kuma an kama su da hujjoji da ke nuna cewa su ne suka aikata kisan in ji rundunar ‘yan sandan.

Kwamishinan rundunar ‘yan sanda na Imo Ahmed Barde ya yaba wa jami’an nasa bisa kokari da suka yi wajen kama mutanen da suka kashe ‘yan sandan.

Ya kuma bukaci al’umma ta bai wa ‘yan sanda hadin kai wajen gano maboyar bata-gari a duk inda suke.

Gwamnatin Najeriya dai ta ayyana kungiyar IPOB a matsayin haramtacciya tare da gargadin ‘yan kasar kar su shige ta.

legit.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp