fidelitybank

‘Yan sanda sun damke dan ta’adda a Jigawa

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta cafke wani mutum mai suna Abdulkadir Alhassan mai shekaru 42 da haihuwa wanda ya dade yana ta’addanci a jihar da kuma jihar Kano.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.

Ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar Talata a kauyen Sabon Sara da ke karamar hukumar Ringim.

Shiisu ya bayyana cewa wanda ake zargin shahararren dan fashi da makami ne kuma mai garkuwa da mutane wanda aka gurfanar da shi a gaban kuliya bisa laifukan fashi da makami.

“Wanda ake zargin ya yi tsallen bada belin kwanan nan a kan laifin hada baki da kuma fashi da makami a kotun majistare Babura,” in ji shi.

Ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin yin garkuwa da mutane da dama daga jihohin Jigawa da Kano.

Yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa laifin karbar miliyoyin naira daga iyalan wadanda abin ya shafa a matsayin kudin fansa.

Kakakin ‘yan sandan ya kara da cewa wadanda ake zargin sun bayyana sunan wani dan kungiyarsu mai suna Alhassan Ya’u mai suna Kato dan shekaru 45 a kauyen Dogamare da ke karamar hukumar Ringim.

Za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan bincike.

assu update

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An ceto Mutane 25 da syka kife a kwale-kwalen Sokoto

Hukumomi a jihar Sokoto sun ce, sun samu nasarar...

An fara duba rabon gyaran arzikin Najeriya

Shugaban Hukumar rarraba arziƙin ƙasa RMAFC, Mohammed Shehu, ya...

Kwallaye 6 da aka zurawa Santos a raga ta sanya Neymar ya fashe da kuka

Ɗan wasan tawagar Brazil, Neymar ya fice daga cikin...

Hukumar Shari’a ta magantu kan sadakin dubu 20 da ya yamutsa hazo a Kano

Hukumar shari’a ta jihar Kano, ta ce ba a...

Cutar Mashako ta yi ajalin Yara hudu a Kano

Rahotanni na cewa cutar mashaƙo wadda aka fi sani...

Cin zaben da NNPP ta yi a Kano cuwa-cuwa ne – Ata

Ministan Jiha na Gidaje da Cigaban Birane, Rt Hon...

Mutane kusan 40 sun ɓace sakamakon haɗarin kwale-kwale a Sokoto

Aƙalla mutum 40 ne ake nema bayan haɗarin kwale-kwale...

APC ta yi kwaf daya a zaben cike gurbin Kaduna da Jigawa

Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Jigawa ta yi...

Ba mu yarda da zaben Ghari da Tsanyawa ba – NNPP

Jam'iyar NNPP mai mulkin jihar Kano a arewacin Najeriya...

QPC ta nemi INEC ta soke zaɓen Kano

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta nemi hukumar zaɓe...

Zaɓen Kano: An kama Mutane 288 da tayar da zaune tsaye

Rudunar ƴansandan jihar Kano, ta sanar da kama mutum...

An Kama wakilin jam’iyya da Naira miliyan 25.9 na Siyan Kuri’a

Jami’an tsaro sun kama wani da ake zargin wakilin...
X whatsapp