Jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya, sun dakile wani yunkurin yin garkuwa da mutane a jihar Kaduna a ranar Litinin din da ta gabata, inda suka samu nasarar kwato wata karamar bindiga kirar gida da harsashi guda daya.
“Jami’an ‘yan sanda a Oskolaye da ke yankin Rigasa a cikin karamar hukumar Igabi sun tare wasu ‘yan bindiga uku da ke shirin kai hari kan wani mutum da misalin karfe 6 na safiyar ranar Litinin.
“Sun kama wadanda ake zargin, amma daya daga cikinsu ya jefar da bindigar gida guda daya da harsashi daya kafin su gudu,” in ji kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan a ranar Talata.
Ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN cewa wadanda ake zargin sun tsallake rijiya da baya ne bayan da jami’an ‘yan sanda suka kama su.
Ya kuma ba da tabbacin cewa za a kama wadanda ake zargi da gudu.
Hassan ya yabawa al’ummar jihar Kaduna bisa yadda suke baiwa ‘yan sanda bayanai akan lokaci kuma masu amfani a kokarinsu na kawar da duk wani nau’in miyagun laifuka a jihar.


