Jami’an ‘yan sanda daga rundunar ‘yan sandan jihar Katsina sun yi nasarar dakile yunkurin yin garkuwa da mutane biyu da suka afku a karamar hukumar Faskari da Malumfashi a jihar Katsina, a ranakun 8 da 9 ga watan Mayun 2024.
ASP Abubakar Sadiq Aliyu, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan ya ce ‘yan bindigar sun kai harin farko ne a ranar 8 ga watan Mayu, 2024, bayan sun tare hanyar Funtua zuwa Gusau, a kauyen Unguwar Boka, a karamar hukumar Faskari, Katsina.
A cewarsa, ‘yan ta’addan sun far wa fasinjoji uku ne da ke tafiya a cikin wata motar Golf III, inda suka dakatar da su da karfi da karfin harsasai.
Sai dai Sadiq ya bayyana cewa shirin nasu ya ci tura sakamakon wani dauki-ba-dadi da jami’an sintiri suka yi a yankin.
“Tawagar da jami’in ‘yan sanda na Faskari (DPO) na Faskari ya jagoranta cikin gaggawa suka afka wa ‘yan bindigar, inda suka kubutar da fasinjojin guda uku ba tare da wani rauni ba.
“Wadanda ake zargin sun jikkata an tilasta musu tserewa daga wurin. A yanzu haka ana ci gaba da bincike domin kamo wadanda ake zargin.” Sadiq yace.
Hakazalika, a ranar 9 ga watan Mayu da misalin karfe 12:45 na safe, Sadiq ya ce ‘yan sandan Katsina sun sake samun nasara a lokacin da jami’anta daga
Hedikwatar sashin Malumfashi ya amsa kiran da aka yi masa na nuna damuwa game da harin da aka kai kauyen Gidan-Maga.
Ya ce wasu gungun ‘yan bindiga dauke da bindigogi kirar AK-47 sun afkawa kauyen, inda suka yi garkuwa da mazauna garin guda goma tare da sace shanu goma sha shida.
“Ba tare da bata lokaci ba, DPO na Malumfashi ya tara jami’ansa suka garzaya wurin da lamarin ya faru.
“A wani kazamin fada da ‘yan sandan suka yi, sun yi galaba a kan ‘yan bindigar, inda suka samu nasarar kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su goma.
“Hakazalika, sun kwato shanu goma sha shidan da aka sace, wanda hakan ya tilasta wa wadanda suka jikkata suka sake komawa baya.
“Kwamishanan ‘yan sandan jihar Katsina, CP Aliyu Abubakar Musa, ya yabawa jami’an bisa jarumtaka da kwarewa,” inji shi.
Ya jaddada jajircewar rundunar na tabbatar da tsaro da zaman lafiyar al’ummar jihar Katsina.