Jami’an ‘yan sanda a jihar Katsina, sun ceto Honarabul Ibrahim Tafashiya dan takarar jam’iyyar PDP a shiyyar Kankia a majalisar dokokin jihar a zaben 2023 mai zuwa.
Aan ta’addan sun yi garkuwa da dan siyasar a ranar Asabar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Sufeto Gambo Isah ya ce rundunar ta dauki matakin ne nan take ta samu kiran gaggawar.
Ya ce jami’in ‘yan sandan yankin Kankia, SP Ilyasu Ibrahim ne ya jagoranci ‘yan sandan da ke karkashinsa wajen tunkarar ‘yan bindigar inda suka yi artabu da bindiga mai zafi wanda ya kai ga ceto dan takarar na PDP.
Hakazalika, rundunar ‘yan sandan Katsina ta ce ta kuma ceto Salisu Gide, magatakardar Kwalejin Ilimi ta Isa Kaita, wanda aka yi garkuwa da shi tare da matarsa daga gidan su da ke cikin birnin Katsina.
“Abin takaici, tawagar ‘yan sanda ta kasa ceto matarsa daga maharan,” in ji shi.
Sai dai SP Gambo ya ce ana ci gaba da kokarin kubutar da ita da sauran mutanen da ake garkuwa da su a matsayin ‘yan ta’addar, inda ya ce an ga maharan a wani wuri a cikin karamar hukumar Batsari.


