fidelitybank

‘Yan sanda sun cafke mai shekaru 75 akan laifin yin fyade ga ‘yarsa mai shekara 4

Date:

Rundunar ‘yan sandan Jihar Nasarawa, ta ce, ta kama wani dattijo mai shekara 75 kan zargin yi wa ‘yar ɗan uwansa fyaɗe mai shekara huɗu.

Sanarwar da kakakin ‘yan sanda DSP Ramhan Nansel ya fitar a yau Lahadi ta ce sun kama Isa Nana Okpoku ne bayan wani rahoto da aka kai hedikwatar rundunar ranar Asabar.

Binciken farko-farko da rundunar ta gudanar ya nuna cewa dattijon na zaune da yarinyar a gida ɗaya da ke Daddare a yankin Ƙaramar Hukumar Obi.

“Isa Nana ya yaudari ƙaramar yarinyar zuwa ɗakinsa kuma ya yi lalata da ita,” a cewar sanarwar. “An garzaya da ita asibiti don yin gwaji, inda likita ya tabbatar da cewa lamarin ya faru.”

Sanarwar ta ƙara da cewa Kwamashinan ‘Yan Sanda Maiyaki Mohammed Baba ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike da kuma ɗaukar matakin shari’a a kan wanda ake zargi da zarar an kamamala.

punch news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Hisbah za ta yi wa ‘yan Daban Kano aure

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da wani...

Ganduje ya dawo Najeriya bayan ya shafe wata guda a Landan

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje,...

Barrister Sa’idu ya kama aiki bayan ya maye gurbin Muhyi Magaji

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rantsar...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

Barau zai mayar da filin wasan BUK na zamani

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jami’ar Bayero ta Kano ta yi sabon shugaba

Farfesa Haruna Musa, ya karɓi ragamar shugabancin jami’ar Bayero...

Gwamnatin Kano ta amince Barau FC ta yi wasa a filin Sani Abacha

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kungiyar kwallon kafa...

Gwamnatin Tinubu na takalar Kwankwaso da fada – Buba Galadima

Jigo a jam'iyyar NNPP, kuma na hannun tsohon gwamnan...

Newcastle United ta dauki dan wasan tsakiya Jacob daga Aston Villa

Newcastle United ta sanar da daukar dan wasan tsakiya...

Hisba ta kama ‘yan Mata 62 da zargin aikata baɗala a Kano

Hukumar Hisbah ta kama mutane 62 kan zargin aikata...
X whatsapp