fidelitybank

‘Yan sanda na bincike a kan karar da mawakiya Tiwa ta shigar da Davido

Date:

‘Yansanda sun fara gudanar da bincike kan shahararren mawaƙin nan na ƙasar Davido bayan ƙarar da abokiyar sana’arsa Tiwa Savage ta shigar a kansa, bisa zargin cin zarafinta da kuma yi mata barazana da rayuwarta.

A watan jiya ne tankiya ta ƙara ƙamari tsakanin mawaƙan biyu, bayan Tiwa ta sanya wani hotonta da na mahaifiyar ɗaya daga cikin ‘ya’yan Davido a shafinta na Instagram.

A ƙorafin da ta shigar a wajen ‘yansandan kamar yadda kafafen yaɗa labarai na ƙasar suka ambato, Tiwa ta ce hoton da ta wallafa ya ɓata wa Davido rai, inda ya yi zargin ta yi hakan ne domin ta fusata shi.

Ta yi zargin amsar da Davido ya mayar mata kan hoton “ya yi ta ne cikin rashin girmamawa da ɓacin rai”.

Tiwa ta yi zargin Davido ya riƙa aikamata mutane Legas su jamata kunne “ta bi a hankali” wanda ta ce “hakan ya saɓa al’ada” kuma “barazana ce ga ‘yancinta na rayuwa, da mutuncinta”.

Har yanzu dai Davido bai ce komai ba kan wannan zargi.

Duka taurarin biyu dai sun yanke ƙawancen da ke tsakaninsu a Instagram.

nasarawa news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp