Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa, ta ce ta ci gaba da bincike kan wani matashi da ake zargin ya hallaka kakarsa.
Ƴan sandan sun ce lamarin ya auku ne a ƙaramar hukumar Sule Tantankarkar a jihar ta Jigawa a sakamakon yadda Kakar matashin ta ke yawan tambayarsa yaya jikinsa, shi kuma ya nuna ɓacin ransa cewa baya so amma taki dainawa.
Kakakin ƴansandan jihar Jigawa, DSP Lawan Adam Shiisu ya ce suna tsare da matashin mai shekara 26, kuma ya ce binciken farko-farko da suka gabatar ya nuna cewa yana fama da matsalar ƙwaƙwalwa.
Bugu-da-ƙari DSP Lawan Adam Shiisu kakakin ƴan sandan jihar Jigawa ya ce bayanan da suka tattara sun nuna cewa bai taɓa auka wa wani ba, kuma ya ce za su kai shi asibitin ƴansanda don tabbatar da ikirarin da danginsa suka yi na cewa yana fama da larurar ƙwaƙwalwa.