fidelitybank

‘Yan Sanda ba za su lamunci rikici ba a zanga-zangar ‘yan Kwadago – IGP Kayode

Date:

Muƙaddashin babban sufeton ƴan sanda na kasa, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya bayana damuwa kan zanga-zangar da ƙungiyyin ƙadago suka shirya yi, inda ya yi gargaɗin cewa ƴan sanda ba za su lamunci duk wani abu da zai kawo rikici ba.

Sanarwar da kakakin rundunar ƴan sandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar ta ce ƴan ƙasa suna da ƴancin yin zanga-zanga kamar yadda kundin mulki ya yi tanadi amma dole ne a gudanar da ita cikin kwanciyar hankali.

Rundunar ƴan sandan ta ce a baya irin wannan zanga-zanga tana rikiɗewa ta zama tashin hankali, sabda haka ta ke gargaɗin cewa ba za ta bari a gudanar da duk wani abu da zai kawo matsalar tsaro ba.

ACP Adejobi ya ce duk wani yunƙurin tayar da rikici a lokacin zanga-zangar ƙungiyar ƙwadago zai fuskanci fushin hukuma.

Ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya sun shirya fara zanga-zanga a faɗin ƙasar daga ranar Laraba 2 ga watan Agusta domin nuna rashin amincewa da soke tallafin mai da gwamnati ta yi.

thisday news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp