fidelitybank

‘Yan sanda a Zamfara sun ceto mutane 24 da aka yi garkuwa da su

Date:

Rundunar ƴan sandan Jihar Zamfara ta ceto mutum 24 waɗanda ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a yankin.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan sandan jihar, SP Mohammed Shehu ya fitar, ya ce, tun da farko sun samu labarin harin da ƴan bindigan suka kai kan hanyar Gurgurawa a Ƙaramar Hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara inda ƴan bindigar suka kwashi jama’a da dama.

Daga nan ne jam’ian ƴan sanda da ƴan bijilanti suka bazama cikin daji nemo waɗanda aka sace.

A cewar SP Mohammed, ko da ƴan bindigan suka hangi jami’an tsaro, sai suka soma harbi kan mai uwa da wabi wanda hakan ya ja aka ci gaba da musayar wuta tsakanin jami’an tsaron da ƴan bindigar.

Ya bayyana cewa, bayan wutar da ƴan bindigar suka sha, sai suka gudu suka bar waɗanda suka yi garkuwa da su.

Mutum 14 waɗanda akasarinsu mata ne aka ceto a wurin da lamarin ya faru, sauran mutum goma kuma a yayin da suke gudu neman ɗauki suka samu suka koma ƙauye ba tare da wani rauni ba.

Haka kuma rundunar ta ce, ta ƙwato babura bakwai waɗanda ƴan bindigan ke amfani da su yayin samamen da suka kai.

nnn-news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp