Mazauna Kumbashi na Ƙaramar Hukumar Mariga da ke Jihar Neja a arewacin Najeriya sun samu sauƙi a hare-haren ‘yan fashin daji sakamakon kashe wasu daga cikin maharan da ‘yan sandan jihar suka yi a ranar Alhamis.
Kafar talabijin ta Channels TV ta ruwaito kakakin ‘yan sandan Neja, Wasiu Abiodun, fafatawar da jami’ansu suka yi tare da haɗin gwiwar mayaƙan sa-kai ta haddasa mutuwar ‘yan fashi bakwai.
Mista Abiodun ya ce mazauna yankin ne suka kai musu rahoto bayan sun ga gilmawar ‘yan bindigar, inda su kuma suka far musu tare da fatattakar wasu ɗauke da raunuka.
Sai dai ya ce mutum biyu daga cikin mayaƙan sa-kan sun ji raunuka kuma an kai su Babban Asibitin Kontagora don ba su kulawa.