fidelitybank

‘Yan sanda 7,000: Hukumar kula da ‘yan sanda ta yi karin girma

Date:

Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta amince da karin girma ga mataimakan sufeto-Janar na ‘yan sanda biyu zuwa matsayi na gaba na mataimakan sufeto-Janar.

Haka kuma ta amince da karin girma ga kwamishinonin ‘yan sanda shida zuwa mataimakan sufeto-janar na ‘yan sanda tare da daukaka mataimakan kwamishinonin ‘yan sanda 17 zuwa kwamishinonin ‘yan sanda.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ‘yan jaridu da hulda da jama’a, Ikechukwu Ani a ranar Laraba.

A cewar sanarwar, hukumar ta kuma amince da karin girma ga mataimakan kwamishinonin ‘yan sanda 24 zuwa matsayi na gaba na mataimakan kwamishinonin ‘yan sanda; 49 manyan Sufeto Janar na ‘yan sanda zuwa matsayin mataimakan kwamishinoni.

Ta kuma amince da daukaka matsayin Sufeto Janar na ‘yan sanda 74 zuwa manyan Sufeto da mataimakan Sufiritanda 866.

Hukumar ta dauki wadannan matakai ne a taronta na 13 da ta gudanar a Abuja a ranakun Litinin 20 ga watan Disamba da Talata 21 ga watan Disamba, 2021, kafin daga bisani ta dage zamanta zuwa watan Janairun 2022 domin ci gaba da tattaunawa.

A yayin taron, rundunar ta kuma amince da tabbatar da masu mikamin ASP11 su 7,166 zuwa ASP1 tare da yin la’akari da kararraki 24 na kara girma da suka shafi daidaitawa a lokutan karin girma da sauransu.

leadership news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp