fidelitybank

‘Yan sa-kai biyu ne suka mutu a harin da muka kai Zamfara – Sojoji

Date:

Rundunar sojin sama ta Najeirya ta tabbatar da kai hare-hare ta sama a jihar Zamfara da ke arewacin ƙasar, tana mai cewa dakarun sa-kai biyu sun rasu yayin da take harar ‘yanfashin daji.

A jiya Litinin ne mazauna ƙaramar hukumar Maru suka shaida wa BBC Hausa cewa jirgin yaƙin sojin ya kashe ‘yan sa-kai, yayin da ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta ce mayaƙa 20 aka kashe a lokacin da suke bin sawun ‘yanbindigar da suka kai musu hari da sace wasu mutane.

Kakakin rundunar Ehimen Ejodame ya ce hare-haren da suka kai bayan samun bayanan sirri sun yi sanadiyyar kashe ‘yanbindigar 20.

“A martanin da muka mayar cikin gaggawa ranar 31 ga watan Mayu, dakarunmu sun kashe sama da ‘yanta’adda 20 tare da lalata babura fiye da 21,” a cewarsa yayin wani taron manema labarai kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

“Abin takaici, yayin wannan aiki ne kuma ‘yan sa-kai biyu suka rasa rayukansu kuma wasu biyu suka ji raunuka. Rundunarmu ba ta ji daɗin abin da ya faru ba kan waɗannan jajirtattun mutane kuma muna aiki da hukumomin yankin domin kare rayukan al’umma.”

Sai dai har yanzu mazauna yankin na cewa mutanen da suka mutu a hare-haren kuskuren sun zarta mutum biyu kamar yadda rundunar ta bayyana.

Ƴan sa-kai 20 jirgin sojoji ya kashe a Zamfara – Amnesty

‘Gazawar gwamnati ke sa wasu jami’an tsaron Najeriya samar da makamai ga ‘yanta’adda’

news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp