Ana samun karuwar sayen tikitin jiragen ficewa daga Rasha, tun bayan sanarwar da Putin ya yi kan aike wa karin sojoji 300,000 a Ukraine.
Yanzu haka ba bu tikitin jiragen da ke zuwa Santambul daga Moscow, haka ma wanda ke zuwa birnin Yerevan na Armenia daga Moscow ya kare.
Dama wadannan garuruwa ne da yan Rasha ke shiga ba tare da takardun biza ba.
Ana dari-dari kan abubuwan da za su iya biyowa baya, da suka hada da yiwuwar Shugaba Putin zai iya amfani da dalibai a matsayin mayaka a Ukraine.


