fidelitybank

‘Yan Najeriya za ku ci gajiyar sauya kudi na CBN – Peter Obi

Date:

Ɗan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar adawa ta Labour Party (LP), Peter Obi, ya roƙi ‘yan Najeriya su yi wa gwamnatin Buhari uzuri da kuma Babban Bankin Najeriya (CBN) kan sauya kuɗin ƙasar.

Ɗan takarar ya ce ba Najeriya ce kaɗai ke sauya takardun kuɗi ba kuma hakan yana da “amfani matuƙa” na tsawon lokaci.

“Ina roƙon ‘yan Najeriya su yi wa CBN da gwamnatin tarayya uzuri kuma su yi fatan al’umma da ƙasa baki ɗaya za su ci amfanin sauyin da aka yi,” kamar yadda ya bayyana cikin wasu jerin saƙonni a shafinsa na Twitter.

Sai dai ya yi kira ga CBN da kuma bankunan kasuwanci da su ƙara ƙaimi wajen yawaita sababbin takardun kuɗin ga mutane da waɗanda ba su da asusun banki “don rage wahalhalun da ‘yan uwana ‘yan ƙasa ke ciki, musamman talakawa da waɗanda ke da nisa da bankuna a ƙauyuka”.

Karanta Wannan: Peter Obi zai baku mamaki APC – Babachir Lawal

Shi ma ɗan takarar babbar jam’iyya adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya goyi bayan sauya kuɗin.

A gefe guda kuma, ‘yan Najeriya na ci gaba da shiga tasku wajen neman garin kuɗin da za su yi hada-hada da su, inda suke shafe awanni a kan layi kafin su samu daga bankuna.

Za a daina amfani da tsofaffin takardun N1,000 da N500 da N200 daga ranar 10 ga watan Fabarairu, kodayake CBN ya ce za a ci gaba da sauya tsofaffi da sababbi bayan wucewar wa’adin.

www.legit news.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp