Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa, ‘yan Najeriya da ke kasashen ketare za su iya shiga kasar ba tare da biza ba.
Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta sanar da hakan a ranar Litinin din da ta gabata a wata wasika da ta aike wa dukkan shugabannin ma’aikatu, kamfanonin jiragen sama, masu kula da shige da fice da kuma kwanturolan filayen jiragen sama.
Babban Kwanturolan Hukumar Shige da Fice, Jere Idris, wanda a cikin wata wasika mai dauke da sa hannun DCI BM Lawal, mataimaki na musamman ga Kwanturola Janar (Foreign Desk), ya ba da umarnin a bar ‘yan Nijeriya da ke da fasfo da ya kare su shigo kasar ba tare da tsangwama ba, ya yi nuni da cewa. dole ne a duba fasfo din Najeriya da ya kare don tabbatar da cewa sun fito daga Najeriya da gaske.
“Saboda haka, an bukaci dukkan kamfanonin jiragen sama da su kyale masu fasfo din Najeriya da ya kare su shiga ba tare da izini ko tsangwama ba.
“Bugu da kari, ana kuma kira ga dukkan jami’an diflomasiyyar Najeriya da ke kasashen waje da su mika wadannan bayanai ga kamfanonin jiragen sama da hukumomin kan iyaka na kasashen da suka karbi bakuncinsu domin daukar matakin da ya dace,” in ji sanarwar.