fidelitybank

‘Yan Najeriya sun daina kwarmata masu satar kudin gwamnati – EFCC

Date:

Hukumar da ke yaki da rashawa ta EFCC ta ce, ‘yan Najeriya sun sare da kwarmata bayanai kan wasu satar kudin gwamnati Tarayyar, duk da babban kudin lada da ke tattare da yin hakan.

Shugaban hukumar ta EFCC, Abdullahi Bawa, ya shaida hakan ne a lokacin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a birnin Kwara, wato Ilorin.

Shugaban ya ce akwai bukatar sake jan hankalin mutane da ankarar da su muhimmanci yin haka a kokarin kwato kudaden sata da sake gina tattalin arzikin kasa.

Sai dai hukumar ba ta yi karin haske ko shaida dalilan da suka sa ‘yan Najeriya suka sare da bada bayanan ba.

Tun a shekara ta 2016 gwamnatin Najeriya ta Æ™addamar da shirin kwarmata bayanai da zummar bai wa ma’aikata da É—aiÉ—aikun mutane damar fallasa ayyukan cin hanci da rashawa, ita kuma gwamnati ta saka musu da kuÉ—in lada.

A cewar Ministar Kuɗi ta lokacin, babbar hikimar ɓullo da shirin ita ce taimaka wa yaƙi da rashawa ta hanyar yawaita bankaɗo laifukan da kuma bai wa masu bankaɗowar lada.

Hakazalika a shekara ta 2021, EFCC, ta kaddamar da wata manhaja da za ta ba ‘yan kasar damar daukar hotunan abubuwa ko wuraren da ake aikata laifuka.

Da yake magana da BBC Hausa, Abdulrasheed Bawa ya ce yunƙurin nasu yana cikin shirin nan na kwarmata bayanai da ake Whistle Blower a Ingilishi.

“Duk wanda yake so ya kwarmata mata bayanai don ya samu wani abu zai iya yin hakan a ciki kuma ya bayyana cewa ya yi hakan ne a matsayinsa na mai kwarmata bayanai,” a cewarsa. In ji BBC.

the sun news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp