Hukumar samar da abinci da bunkasa noma ta duniya, ta ce ‘yan Najeriya akalla miliyan biyu da dubu 600, a jihohin Borno da Sokoto da kuma Zamfara da kuma babban birnin kasar Abuja, na iya fuskantar matsalar rashin abinci a tsakanin watan Yuni da Agustan 2024.
Wakilin hukumar, Dr. Abubakar Suleiman ne, ya bayyana haka yayin gabatar da bayani na gargadin wurwuri ranar Juma’a a Abuja.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa bayanin, wani bangare ne na rahoto a kan tabbacin halin wadata al’umma da abinci, da kuma hasashe game da halin da za a shiga nan gaba.
A cewarsa, halin da ake ciki yanzu ya faru ne bayan wata damuna da ba a saba da ganin irinta ba, wadda aka samu matsaloli da dama, kama daga ta’azzarar halin rashin tsaro kamar rikicin ‘yan ta-da-kayar-baya da na ‘yan fashin daji.