fidelitybank

‘Yan Najeriya na fama da matsanancin rayuwa – Dr Hussaini

Date:

‘Yan Najeriya har yanzu suna fama da matsin rayuwa a lokacin da suke kokarin neman abin rufin asiri, yayin da suke fuskantar tsadar kayan abinci da hauhawar farashi.

Hakan na zuwa ne wata biyar bayan gwamnatin kasar ta fitar da kuɗi har naira biliyan 72 domin shirin rage raɗaɗi, sakamakon matsin rayuwar da aka shiga bayan cire tallafin man fetur a watan Mayun bara.

Wani kwararre kan al’amuran ci gaban duniya, Dr Hussaini Abdu ya yi wa BBC bayani kan dalilin da ya sa shirin rage radadin bai cimma buri ba.

A cewar sa tallafi ba ya magani kai tsaye musamman kan abin da ya shafi tattalin arziki saboda “ana yi ne domin a cikin takaitaccen lokaci a rage nauyi, kafin ka farfado ka nemi abin yi.”

Kwararren ya ce mafi yawan al’umma sun ce an raba kayan tallafi amma ba su gani a kasa ba dalilin da ya sa ya ce ya kamata a ce an dauki lokaci ana aiwatar da tsarin tare da ware adadin da za a rika bai wa mutane.

Dr Abdu ya soki tsarin da aka bi wajen yin rabon kayan tallafin da ya ce irin tsarin ba ya “taɓa maganin talauci a ko ina.”

“Abu ne aka yi ba kan tsari ba, saboda haka ba yadda za a yi a ce ya yi maganin irin wannan abun.” in ji Dr Abdu.

Ya kara da cewa har yanzu akwai jihohin da ko “ƙwandala” ba su gani ba duk da iƙirarin gwamnati cewa ta fitar da kuɗaɗe ga jihohi domin rage raɗaɗin da al’umominsu ke fuskanta.

daily post nigeria today news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Zan cigaba da sa yawan jini ga maƙiya Tinubu – Wike

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya sha alwashin...

Tinubu zai magantu a kan ranar Dimokradiyya

Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, zai yi jawabi ga...

A shirye nake na mutu don nasarar APC a 2027 – Orji Kalu

Sanatan Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya bayyana...

Bayan hutun Sallah Tinubu zai koma Abuja

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu na kan hanyarsa ta komawa...

Mutane 570 aka kashe a Najeriya cikin watan Afrilu – Rahoto

Hukumar kare haƙƙin ɗan'adam a Najeriya ta ce, adadin...

PDP ba za ta mutu ba duk da rikicin cikin gida – Wike

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya ce...

Sojoji sun kashe riƙaƙen ɗan bindiga Guddel a Kaduna

Sojoji sun yi nasarar kawar da fitaccen shugaban ‘yan...

Fadar shugaban ƙasa ta yi kakkausar gargaɗi a kan Ndume

Fadar shugaban kasa ta yi kakkausar gargadi ga dan...

Kare Ya Kashe Ragon Layya: Mai ƙwacen waya ya kashe Sojin ruwa a Kaduna

Wani mai ƙwacen waya ya kashe wani soja bayan...

Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram da dama

Da sanyin safiyar ranar Litinin, dakarun rundunar Haɗin kai...

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...
X whatsapp