fidelitybank

‘Yan Najeriya mu tashi tsaye mu yi gyara – Ortom

Date:

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bukaci ‘yan Najeriya da su tashi tsaye wajen ganin sun yi aiki tare domin ci gaban kasar.

Gwamna Ortom ya ba da wannan cajin ne a ranar Asabar 3 ga watan Disamba, 2022 a Fatakwal, jihar Ribas jim kadan bayan ya samu lambar yabo mafi girma a jihar, ‘Grand Serbice Star of Rivers State’ GSSRS.

Ya bayyana cewa a wannan lokaci na musamman a tarihin kasar nan da ake fuskantar kalubale a fannin tattalin arziki, zamantakewa, siyasa da tsaro, abin da kawai ake bukata shi ne jama’a su nuna kishin kasa domin ceto kasar.

Gwamnan ya yaba wa hikimar Gwamna Nyesom Wike da al’ummar Jihar Ribas da suka nuna wa Najeriya hanya ta wannan lambar yabo, wadda ta sa aka karrama jama’a a shiyyoyi shida na kasar nan.

Ya ce hakan ya nuna imanin gwamna Wike da al’ummar jihar kan hadin kan Najeriya.

A cewar Gwamna Ortom, “Idan kowane mutum a Najeriya zai yi tunani kamar Gwamna Wike, kasar za ta kasance mai girma kuma za ta dauki matsayinta a matsayin jagoran Afirka kuma babbar Afirka.”

Gwamna Ortom ya yi kira ga al’ummar kasar da cewa, a yayin da al’ummar kasar ke shirin shiga babban zaben shekara mai zuwa, kada su kalli jam’iyyun siyasa, kuma kada su kalli kabilanci, sai dai yadda za mu iya ceto kasarmu Nijeriya, mu mai da ta fiye da yadda take a yau.

Gwamnan ya yi kira ga wadanda aka karrama da su kai sakon da Gwamna da al’ummar Jihar Ribas suka isar zuwa jihohinsu da yankunansu domin jama’a su yaba da bukatar yin aiki tare domin hadin kai da ci gaban kasa.

bbc naija news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnan Kano ya kori mataimansa na musamman kan belin Danwawu

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da...

Tsohon Minista a mulkin Buhari ya mutu

Allah ya yi wa tsohon ministan noma da raya...

Kashi 70 na yankin Bukuyum ta Kudu na ƙarƙashin ƴan Bindiga – Ɗan majalisa

Rahotanni daga yakin ƙaramar hukummar Bukuyum na jihar Zamfara...

Goodluck ya fi dacewa ya zama dan takara a 2027 – Lamido

Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce Tsohon...

An gargadi al’umma su yi taka tsan-tsan da ambaliyar ruwan sama

Yayin da ake ci gaba da fuskantar saukar ruwan...

Gwamnatin Tarayya za ta gina hanyar sufurin jirgin ƙasa a Kano

Gwamnatin Tarayya ta ce, za ta samar da titin...

Abin da ya sa muke ci gaba da tsare Sowore – Ƴansanda

Kwamishinan ƴansanda mai kula da sashen kai ɗauki na...

INEC za ta bai wa ɗaurarru damar kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓuka

Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta ta duba yiwuwar bai...

Mai ya jawo Matan Zamfara su ka yi zanga-zanga

Ɗaruruwan mata ne tsofaffi da masu shawarya suka gudanar...

Aƙalla mutane 24,000 ne suka ɓata saboda Boko Haram a Najeriya

Kungiyar Agaji ta Red Cross ta bayyana cewa aƙalla...

‘Yansanda ku gaggauta sakin Sowore – Obi

Tsohon ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter...

PDP ta gargaɗi mambobinta kan goyon bayan Tinubu

Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta gargaɗi...
X whatsapp