fidelitybank

‘Yan Najeriya miliyan 82 za su fuskanci matsalar yunwa – MDD

Date:

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin cewar ‘yan Najeriya miliyan 82, kimanin kashi 64 na ‘yan ƙasar ka iya fuskantar matsalar yunwa nan da shekarar 2030.

Haka kuma MDD ta yi kira da gwamnatin ƙasar ta magance matsalar sauyin yanayi da matsalar ƙwari da sauran abubuwan da yi wa harkar noma barazana.

Jaridun Najeriya sun ambato jami’in Majalisar Dinkin Duniyar, Taofiq Braimoh – wanda ya wakilci kodinetan ayyukan jin ƙai na hukumar abinci da ayyukan noma na majalisar – na bayyana haka lokacin da yake jawabi kan matsalolar ƙarancin abinci a taron ƙaddamar da shirin bunƙasa ayyukan noma na ‘CropWatch’ a birnin Abuja.

Mista Braimoh ya ce akwai buƙatar gwamnatin Najeriya ta ɗauki matakan da suka dace cikin gaggawa don magance matsalar.

“Gwamnatin Najeriya tare da haɗin gwiwa masu ruwa da tsaki, sun gudanar da bincike na shekara-shekara da suka saba gudanarwa kan abinci. Sakamakon binciken ya tayar da hankali, kimanin mutum miliyan 82 ne za su fuskanci yunwa nan da 2030,” kamar yadda Jaridun ƙasar suka ambato Braimoh na bayyanawa.

Ya ci gaba da cewa matsalar rashin abinci da ƙasar ke fama da shi, baya rasa nasaba da matsalar sauyin yanayi da duniya ke fama da ita, da matsalar ƙwari da wasu abubuwa da ke yi wa harkar noma barazana a ƙasar.

Hasashen na Majalisar Dinkin Duniyar na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsalar tsadar abinci, lamarin da ya tilasta wa gidaje da dama haƙura da sayen abincin da suka saba ci.

A cikin rahotonta baya-bayan nan, hukumar ƙididdigar ƙasar ta ce farashin abinci a ƙasar ya ƙaru zuwa kashi 40.66 a watan Mayu, matakin da aka jima ba a ga irinsa ba.

nnnnews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp