Gwamnatin tarayya ta fitar da wasu shawarwari ga al’ummarta masu zuwa ƙasashen Amurka da na Tarayyar Turai.
A wani taron manema labaru da ya gudana yau Litinin a Abuja, ministan yaɗa labarai, Lai Mohammed, ya ce, an fitar da shawarwarin ne bayan rahotanni na kai wa ƴan Najeriya hari da ƙwace masu kaya a ƙasashen waje, ciki har da birnin London.
Mohammed ya ce, ana karɓe wa mutanen da suka fito daga Najeriya kaya, ciki har da kuɗi da fasfo na tafiye-tafiye.
Saboda haka ya ce, ya kamata ƴan Najeriya da ke tafiye-tafiye zuwa ƙasashen nahiyar Turai da Amurka su rinƙa yin taka-tsantsan.
A kwanakin baya ne ƙasashen Amurka da Birtaniya da kuma wasu daban suka gargaɗi al’ummarsu daga zuwa Najeriya saboda rashin tsaro da ake fama da shi.