fidelitybank

‘Yan Najeriya ku yi hakuri da gwamnatin mai gidana – Matar Tinubu

Date:

Matar shugaban kasa Bola Tinubu, Oluremi, ta bukaci ‘yan Najeriya su yi hakuri da gwamnatin mijinta.

Uwargidan shugaban kasar ta ce gwamnatin da Tinubu ke jagoranta na aiki tukuru don ganin an bunkasa kasa da tattalin arziki.

Oluremi ta ce yana bukatar jajircewa da sadaukarwa sosai shi ne zai wadata ga ‘yan Najeriya.

Ta yi wannan roko ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Alhamis yayin da ta karbi bakuncin Sanatocin da ke wakiltar kananan hukumomin uku na jihar Legas.

“Gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ta kuduri aniyar barin gado ga tsararraki har yanzu ba a haife su ba. Wannan yana bukatar sadaukarwa da jajircewa,” inji ta.

Ta kuma sake nanata kiran da ta yi na ‘yan majalisar da su samar da dokar da za ta hukunta masu garkuwa da mutane a kasar.

Uwargidan shugaban kasar, wacce ta taba wakiltar Legas na tsawon shekaru 12 a majalisar dattawa, ta yi kira ga ‘yan majalisar da su jagoranci aiwatar da dokokin da suka shafi tsaro domin dakile yaduwar wannan laifi.

Tun da farko, shugaban tawagar, Sen. Adetokunbo Abiru, mai wakiltar Legas ta Gabas, ya ce sun zo ne domin yi wa uwargidan shugaban kasa gaisuwar ban girma.

Airu, Shugaban kungiyar Sanatocin Kudu, ya ce sauye-sauyen da Shugaba Tinubu ya yi na kan gaba wajen dora al’ummar kasa kan turbar tattalin arziki da ci gaba mai dorewa.

the nation newspaper 
today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp