A ranar Litinin ne shugaba Bola Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya da su canza tunaninsu na neman kudi.
Ya yi wannan nasihar ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, karkashin jagorancin shugabanta, Archbishop Daniel Okoh, a fadar gwamnati da ke Abuja.
“Bari mu tattauna domin Allah wadai da al’umma ba shi ne ke sa kowane dan kasa zama nagari ba. Dole ne mu gargadi ’yan Najeriya da su canja tunani kada su yi kud’i ko su bauta musu. Na yi imani za mu isa Ƙasar Alkawari, kuma Nijeriya za ta bunƙasa,” inji shi.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ya fitar, Tinubu ya kuma shaida wa shugabannin Kiristocin cewa gwamnatinsa ba ta ja da baya, inda ya yi alkawarin yin adalci ga daukacin ‘yan Najeriya.
“Muna nan don saurare, kuma idan kun lura da wani gazawa a cikin gwamnati na, ku sanar da mu. Ina nan a yau saboda addu’o’in ku da yardar Allah Ta’ala. Abin da na kalubalanci kaina na yi kowace rana shi ne yin adalci ga daukacin ‘yan Najeriya,” ya kara da cewa.