Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta gargadi ‘yan Najeriya da su daina amfani da abubuwan kara kuzari da a ka fi sani da aphrodisiac, domin burge abokan zamansu mata, inda ta jaddada cewa shan irin wadannan abubuwan na iya haifar da shanyewar jiki ko kuma mutuwa kwatsam.
Gargadin ya zo ne a daidai lokacin da NAFDAC ta bayyana cewa hukumar ta kama jabun magunguna da haramtattun magunguna da a ka haramta na Naira biliyan 3 da kuma kayayyakin abinci marasa kyau da hukumar ta kama a kwanan baya a harabar kasuwar ta Legas.
Ta kara da cewar, akalla tireloli 20 na irin wadannan haramtattun kayayyaki su ka kwashe su, kuma jami’an hukumar na ci gaba da bincike domin tabbatar da doka karkashin jagorancin Kingsley Ejiofor.
Ya ce wasu daga cikin magungunan da a ka kame a harabar baje kolin kasuwanci na kara kuzari ne.
Hukumar ta kuma gargadi ‘yan Najeriya da su rika lura da abin da su ke ci, inda ta bayyana cewa rashin kulawa na iya yin illa ga lafiyarsu.
Darakta Janar, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta ba da wannan gargadi a cikin sakonta na Kirsimeti da na sabuwar shekara ga ’yan Najeriya, inda ta koka kan yadda a ke amfani da kwayoyi masu kara kuzari da a ka fi sani da ‘manpower’ a harshen gida, a kasuwannin Najeriya.
A cewar Adeyeye, galibin magungunan da ke kara kuzari ba su da rijista da NAFDAC.
A cikin wata sanarwa da mai ba da shawara kan harkokin yada labarai na NAFDAC, Sayo Akintola, ya fitar a Legas ranar Lahadi, Adeyeye ya koka da cewa maza da yawa sun mutu ta hanyar amfani da kwayoyi masu kara kuzari kuma ‘yan uwansu za su dora alhakin mutuwarsu a kan wasu bokaye masu gaskiya a kauyen.