Tsohon shugaban mulkin soja a Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar ya ja hankalin ‘yan kasar kan muhimmancin kare ‘yancinsu da kuri’arsu a babban zaben 2023.
Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, ya yi wannan kira ne a lokacin da yake shirin gudanar da taron sa hannu a yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin ‘yan takara na jam’iyyun siyasa gabannin yakin neman zabe.
Taron zai kuma kunshi sauran masu ruwa da tsaki inda za a sanya hannu a rukuni biyu.
Na gabanin fara yakin neman zabe da kuma gab da babban zaben kasar da za a gudanar a shekara mai zuwa.
A can baya dai an saba kulla irin wannan yarjejeniya tsakanin ‘yan takara kafin zabe.
Sai dai a wannan lokaci an ga sauyi, saboda tabbatar da cewa komai ya tafi a cikin lumana.