Shugaba Muhammadu Buhari, ya kira ga ‘yan kasa da su sanya bukatar kasa a farko, sannan su rike addini wajen samun hadin kai a tsakani.
A wata sanarwar sakon barka da sallah ga al’ummar musulmi a Najeriya da maitaimaka wa shugaban na musamman kan harkokin yada labaru, Malam Garba Shehu ya fitar, Shugaba Buhari ya ce ‘in har da muna amfani da koyarwar addini, da mun sami mafita kan yawancin matsalolin da muke fuskanta a yanzu.”
A cewar Shugaban ya kamata addini ya zamanto a matsayin abin a za a yi amfani da shi wajen yin abu mai kyau ga kasar nan.
Ya kara da cewa satar kudin kasa da wasu jami’an gwamnati ke yi, wata manuniya ce ta yadda mutane ka barin koyarwar addini.
Shugaban ya kara da cewa ”mutane a yanzu basa soron Allah, inda suke sanya abubuwa su zamanto masu wahala ga wasu”.
Haka kuma ya ce ”shugabanni sukan watsar da shan rantsuwa da suka yi yayin shiga ofis ta hanyar karkatar da kudaden da aka tanada domin walwalar ‘yan kasa zuwa aljihunansu.
A kan matalar tsaro da kuma tsadar rayuwa da kasar ke fuskanta, shugaban ya sha alwashin cewa ba zai gajiya ba har sai ya samar wa ‘yan Najeriya mafita, inda yace yana sane da irin wahalhalun da suke ciki, kuma zai yi maganin hakan nan ba da jimawa ba.
A karshe Shugaban ya taya musulman Najeriya da ma na duniya baki daya murnar bikin sallar layya.