Rundunar sojin kasa ta roki jama’a da su daina yada hotunan dakarunta da suka rasa ransu a hare-hare ta shafukan intanet.
Hukumomin sojin suna magana ne kan wani harin kwanton-bauna da wasu ‘yan bindiga suka yi wa sojoji da ke kan hanyarsu ta kai dauki a yayin harin da ‘yan bindiga suka kai kan wasu ma’aikata ‘yan China masu hakar ma’adanai a yankin karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja, ranar Laraba 29 ga watan Yuni, 2022.
Sanarwar da darektan hulda da jama’a na rundunar sojin kasa, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, ta ce, duk da cewa jama’a suna da ‘yancin amfani da kafafen intanet, to amma akwai bukatar su rika hakuri wajen yada hotunan jami’an da aka kashe har sai an sanar da iyalai da ‘yan uwansu.
Haka kuma rundunar ta bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da mara wa jami’nta baya a yakin da suke yi da wadanda ta kira makiyan kasar.
Idan dai ba a manta ba, a lokacin harin ‘yan bindigar sun sace ma’aikata ‘yan kasar China akalla hudu, tare da kashe jami’an tsaro akalla shida wadanda suka kunshi ‘yan sanda da sojoji da kuma ‘yan sintiri na bijilante, kamar yadda ‘yn sanda suka tabbatar wa BBC.
Sai dai kuma wata majiya ta sheda wa BBC, cewa sojoji 4 da ‘yan sandan sintiri (mobile) 4 da kuma ‘yan kungiyar sintiri biyu aka kashe a harin.