Hukumar Kula da shaidar ɗan ƙasa (NIMC), ta bayyana damuwarta kan yadda wasu ƴan ƙsar ke sayar da bayanansu, ciki har da lambar shaidar ɗan kasa (NIN), domin samun kuɗi.
Wannan na zuwa ne bayan sanarwar da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta fitar cewa wasu mutasa na biyan mutane naira 1500 zuwa 2000 don karɓar bayanansu sannan su sayar da su ga wasu kamfanonin hada-hadar kuɗi a kan naira 5000.
A wata sanarwa da shugaban sashen hulɗa da jama’a na hukumar, Dr. Kayode Adegoke ya fitar, sanarwar ta ce ba za ta ɗauki alhakin duk wani bayani da mutum ya bayar da kansa ko ta wani ba, musamman idan hakan ya kasance domin samun kuɗi ko riba.
NIMC ta bayyana cewa wannan lamari yana da matuƙar haɗari ga tsaron ƙasa da kuma tsaron rayuwar masu NIN ɗin wanda dalilin hakan ne hukumart gargaɗi ƴan Najeriya da kada su dinga bayar da bayanansu ga kowanne mutum da ba ma’akacin hukumar ba.
Hukumar ta NIMC ta sha jan kunnen al’umma a baya cewa kada su rika bayyana lambar NIN dinsu ga kowanne mutum sai da ga ma’aikacin NIMC ko kuma waɗanda hukumar ta amince da su