Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Sanata Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa, ba za su yi nadamar zaban shi a kan karagar mulki a zaben 2023 ba.
Da yake jawabi a Kaduna ranar Talata a taron shiyyar Arewa maso Yamma, dan takarar shugaban kasar ya ce, “Ina so in tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa zabe na a matsayin shugaban kasar nan zai zama tirjiya ga dukkan kalubalen da ‘yan kasar ke fuskanta. ”
Ya kuma gargadi duk masu tayar da zaune tsaye da su nemo hanyoyin da za su bi, yana mai tabbatar da cewa duk wanda bai yarda da zaman lafiya da hadin kai da ci gaban kasa ba, ba zai samu sauki ba idan a karshe ya zama shugaban kasar.
Ya kara da cewa kalubalen tsaro da ake fuskanta yanzu zai zama tarihi kuma ‘yan Najeriya na iya gudanar da harkokinsu na yau da kullun.
Ya bayyana cewa, “Gwamnatina za ta yi duk mai yiwuwa wajen samar da ayyukan yi, ta yadda matasanmu za su fahimci halin da suke ciki. Za a ba da duk wata dama ta baiwa manoman mu yanayin da za su iya komawa gona da abubuwan da suka dace don bunkasa noma a kowane bangare na kasar nan”.
Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su shirya musu katin zabe, yana mai cewa su shirya zaben ‘yan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben badi.
Tun da farko Gwamna Nasir El-Rufai ya godewa al’ummar yankin Arewa maso Yamma da suka zo Kaduna domin gudanar da gangamin, ya kuma umarce su da su tabbatar sun zabi jam’iyyar APC a dukkan matakai a zaben badi.