fidelitybank

‘Yan Najeriya 2,090 za su fara dawowa gida Najeriya daga Ukraine

Date:

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa kimanin ‘yan Najeriya 2,090 ne za su dawo gida Najeriya daga kasar Ukraine a ranar Alhamis, bayan farmakin da sojojin kasar Rasha suka kai a Ukraine.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa, wadannan ‘yan Najeriya da suka makale sun nuna sha’awar komawa gida, bayan sun tsere zuwa kasashen Hungary, Poland, Romania, da Slovakia.

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba a Abuja, babban sakataren ma’aikatar harkokin wajen kasar, Gabriel Aduda, ya bayyana cewa, jiragen da aka yi hayar za su tashi ne a ranar Laraba 2 ga Maris, 2022, domin dauko ‘yan Najeriya da aka kwashe zuwa gida.

Ya ce: “Aiki da hanyar da kamfanonin jiragen suka yi sune kamar haka: Max Air zuwa Romania mutum 560, Air Peace zuwa Poland mutane 364 da Air Peace zuwa Hungary 360.

Aduda ya kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatin tarayya na aiki ba dare ba rana domin dawo da ‘yan Najeriya gida lafiya.

network news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp