Al’ummar kasar Morocco sun kagu da ganin an buga wasan kusa da na karshe da kasarsu za ta kara da Faransa idan anjima.
Morocco, ta zamo kasar Larabawa kuma ta Afirka ta farko da ta kai zagayen kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya.
Morocco ta kai wannan matakin ne bayan ta doke Portugal a makon da ya wuce, nasarar da ta ba wa mutane da dama mamaki.
A birnin Casablanca, masu shagunan shan gahawa sun shirya shagunansu tsaf bayan sun jera kujeru da tebura da kuma hada kayan shayi kala-kala don masu kallon wasan da za a buga.
Ana ta sayar da tutoci da kuma rigunan ‘yan kwallo a yawancin biranen kasar.
Masoya kwallon kafa a kasar sun ce ba su taba tsammanin za su ga wannan rana ba, sannan kuma wannan nasara bata kasar bace ta illahirin nahiyar Afirka da ma kasashen Larabawa ce.
Yawancin ‘yan kasar na fatan kasar tasu ta samu nasara a kan Faransa.