fidelitybank

‘Yan majalisun da suka bar ofishin su sun wawure komai gatta Talabijin ba su bari ba – Oshiomhole

Date:

Tsohon Gwamnan Jihar Edo kuma Sanata mai wakiltar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya bayyana kaduwarsa kan abin da ya kira matakin barnatar da kadarorin Majalisar Dokoki ta kasa da ‘yan majalisar suka yi.

Oshiomhole ya bayyana cewa, duk da kasancewar jami’an tsaro maza da mata, sai da wasu Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai na baya-bayan nan suka wawure talbijin, katifu da kujeru.

Oshiomhole ya bayyana hakan ne a lokacin da ya bayyana a gidan talabijin na Channels Television na Sunday Politics.

A cewarsa, tsoffin ‘yan majalisar sun bar ofisoshinsu ne a ruguje da ramuka a bango, inda suka ce sai da ya biya ya gyara ofishinsa kafin amfani da shi.

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya jaddada cewa an kuma barnata a ofisoshin da wasu manyan jami’an majalisar da suka bari, wadanda ya ki bayyana sunayensu.

“Bari in fada muku abu daya da majalisar kasa ba ta magana a kai kuma ban san dalilin da ya sa wadanda ke da hakkin yin magana ba sa magana a kai.

“Na yi matukar kaduwa da matakin barnatar da kadarorin Majalisar Tarayya. An kwashe gidajen Talabijin, an kwashe katifu, an kwashe kujerun Sanatoci. Sai da na yi amfani da kudina, wani kuma ya yanke shawarar kawo mani na’urar bugawa, don ba ni kwamfutar da zan yi amfani da ita a ofishina. Sai da na sayi kafet na biya kudin gyara shi. Dole ne in biya wasu matasa don tsaftace ofishin don mayar da sabon kafet. Sai da na biya na gyara ofishina. Zan kawo muku rasit.

“Ba zan iya fahimtar dalilin da ya sa da kuma yadda majalisar dattawan da ta zauna a ranar Lahadi kafin a kaddamar da mu a ranar Talata mai zuwa, kuma matakin barna ya faru, kuma muna da daruruwan jami’an tsaro maza da mata a majalisar dokokin kasar. Ba zan iya fahimtar abin da ya faru ba. Kuna samun ramuka a bango, har ma a ofisoshin manyan hafsoshin majalisar dattawa, wadanda ba zan iya ambata ba.

“Mutane sun gaya min cewa akwai irin wannan barna a majalisar wakilai,” in ji Oshiomhole.

bbc nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp