‘Yan majalisar wakilai uku daga jihar Imo sun fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki tare da magoya bayansa sama da 3,000.
Gwamnan Imo, Hope Uzodinma ne ya tarbi wadanda suka sauya sheka zuwa jam’iyyar a dandalin Rear Admiral Ndubuisi Kanu, Owerri, babban birnin jihar a ranar Litinin.
‘Yan majalisar tarayya ciki har da Hon. Ikenna Elezieanya, Hon. Bede Ekeh, Hon. Henry Nwawuba da wasu mutane da dama sun yi wannan yunkuri gabanin zaben gwamnan jihar da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba.
A jawabinsa na maraba, Gwamna Uzodinma mai neman sake tsayawa takara a karo na biyu, ya tabbatar wa ‘yan jam’iyyar APC daya ce, ya ce ko tsoho ko sabo ‘ya’yan jam’iyya daya ne.
A cewar Gwamnan, “Babu sabon dan jam’iyyar APC kuma babu tsohon dan jam’iyyar APC, mu daya muke”.
Gwamna Uzodinma ya kuma bukaci daukacin ‘ya’yan Imo maza da mata ba tare da la’akari da jam’iyya ba da su hada kai da shi domin samar da ci gaba ga Ndi Imo.