‘Yan majalisar dokokin jihar Ribas su 26 sun janye sanarwar tsige gwamna Siminalayi Fubara.
Wannan yana kunshe ne a cikin sanarwar janyewar da aka karanta a gidan a ranar Laraba.
Sun ce sun dauki matakin ne saboda mutunta shugaba Bola Tinubu wanda a ranar Litinin din da ta gabata ya kira taron sulhu tsakanin bangarorin da ke rikici da juna.
‘Yan majalisar 26 da ke biyayya ga tsohon Gwamna Nyesom Wike sun zauna a harabar majalisar a safiyar Laraba inda aka karanta hukuncin.
DAILY POST ta ruwaito cewa a ranar Litinin ne shugaba Tinubu ya kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Fubara da magabacinsa, Wike.
Rikicin dake faruwa a jihar dai ana zargin ya samo asali ne daga rikicin mulki tsakanin gwamnan da Wike wanda a halin yanzu yake rike da mukamin ministan babban birnin tarayya.


