‘Yan majalisar Birtaniya 220 sun nemi gwamnatin ƙasar ta amince da ƙasar Falasɗinu cikin wata wasiƙa da suka aika wa Firaminista Keir Starmer.
Suna son ƙasar ta bi sawun Faransa – da wasu ƙasashe na MDD – wajen amincewa da ayyana ‘yancin cin gashin kai na ƙasar Falasɗinawa.
Wakilin BBC ya ce yunƙurin wani mataki ne da ke nuna suka da Allah wadai da abin da Isra’ila ke yi a Gaza yayin da ake fama da bala’in yunwa a zirin.
Sai dai Firaminista Starmer ya ce duk wani yunƙuri na amincewa da ƙasar Falasɗinu mai cikakken ‘yanci sai ya jira ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta a Gazan.