fidelitybank

‘Yan majalisar Andulusiya sun amince da kasafin kudin 2022

Date:

‘Yan majalisar kasar Andulusiya sun amince da kasafin kudin kasar na 2022 bayan da ‘yan majalisar kasar su ka goyi bayan wani sabon gyara game da yarukan marasa rinjayen kasar.

Yin la’akari da kaso na farko na Yuro biliyan 70 kwatankwacin (dala biliyan 79.11) daga asusun dawo da COVID-19 na Tarayyar Turai, kasafin 2022 ya ƙunshi adadin kashe kuɗi na tarihi kusan € biliyan 250 kwatankwacin $ biliyan 282.55).

Gwamnatin Spain ta tabbatar da cewa kashe kuɗin wanda a ka shigar ya dace da raguwar gibin jihar. Hasashen karuwar kashi 7% na GDP na shekarar 2022, wani abu da masana da yawa ke kallo a matsayin kyakkyawan fata, da gwamnati ta ce za shigar da bayanan adadin kudi a shekara mai zuwa.

Bangaren kashe kudaden ciki harda masu karbar fansho da na walwalar ma’aikatan gwamnatin wanda za su ga adadin kuɗin da suke yi na wata-wata ya karu da akalla kashi 2% a shekara mai zuwa.

Domin haɓaka fannin al’adu kuwa, duk wanda ya cika shekaru 18 a kasar, za a ba shi kyautar Yuro 400 kwatankwacin dala 452 domin kashewa kan wajen sayen littattafai ko yin wasu ayyuka kamar bangaren kide-kide ko wasan kwaikwayo.

Kusan mutane 70,000 masu shekaru 18 zuwa 35 suma za su iya cin gajiyar tallafin har zuwa Euro 250 kwatankwacin dala 283 a cikin kowane wata wanda gwamnati ke bayarwa domin taimakawa masu karamin karfi su sami kudin biyan haya a kasar ta Spain.

Haka kuma, karin haraji na kan gaba ga wasu. Tun daga shekara mai zuwa lokacin da kasafin ya fara aiki, manyan kamfanoni za su biya mafi ƙarancin kashi 15% na haraji, adadin da ya yi daidai da kudurin G20 na harajin kamfanoni.

Kasafin kudin dai ya samu amincewar karshe ne a ranar Talata bayan da ‘yan majalissu 281 suka kada kuri’ar amincewa da gyara na karshe sannan 62 kawai suka ki amincewa da shi.

Yarjejeniyar tana nuna ƙarin kwanciyar hankali ga gwamnatin haɗin gwiwa ta farko ta Spain karkashin jagorancin Socialists da Unidas Podemos. Tsakanin 2015 zuwa 2019.

Wannan shi ne karo na farko tun shekara ta 2014 gwamnatin Spain ta yi nasarar zartar da kasafin kudin shekara biyu a jere.

Firayim Ministan Spain Pedro Sanchez ya yaba da yarjejeniyar a matsayin wani muhimmin bangare na murmurewa ga kasar ta Andulusiya.

the punch newspaper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp