Wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka, sun buƙaci gwamnatin Najeriya ta saki babban jami’in kamfanin hada-hadar kudin intanet na Binance, Tigran Gambaryan da hukumomi sukae tsare shi a gidan yari na Kuje da ke Abuja, bayan da suka ziyarci jami’in a ranar Laraba.
A wani hoton bidiyo da ya sanya a shafinsa na X, ɗan majalisar wakilai French Hill tare da takwararsa Chrissy Houlahan, ya ce a lokacin da suka ziyarci Gambaryan, wanda ɗan Amurka ne, sun ga cewa yana fama da wasu matsaloli na rashin kyawun gidan ajiya da gyaran halin.
Ƴan majalisar dokokin na Amurka, sun yi zargin cewa an hana Gambaryan samun kulawar da ta dace ga lafiyarsa, inda ya kamu da cutar zazzaɓin cizon sauro da kuma ta sanyin haƙarƙari wato (nimoniya).
Sun kuma buƙaci ofishin jakadancin Amurka da ke kasar nan da ya nemi a saki jami’in bisa dalilai na jinƙai da rashin laifi, saboda mummunan halin da gidan yarin yake ciki.
A watan Fabarairu ne aka kama Tigran Gambaryan tare da abokin aikinsa Nadeem Anjarwalla, mai takardar shedar ɗan ƙasar Birtaniya da Kenya.
Sai dai takwaran nasa Nadeem Anjarwalla ya tsere daga hannun hukomomin tsaro.
Wannan kiran ya biyo bayan buƙatar da wasu yan majalisar dokokin na Amurka su 18 ne suka gabatar ga Shugaban Amurka Joe Biden domin ya sa baki a saki Mista Gambaryan.