‘Yanmajalisar Wakila biyar sun sauya sheƙa daga jam’iyyar Labour Party (LP) zuwa All Progressives Congress (APC) mai mulkin ƙasar.
Wakilan da suka sauya jam’iyyar a zaman majalisar na yau Alhamis su ne: Esosa Iyawe (jihar Edo), Tochukwu Okere (Ijihar mo), Donatus Matthew (jihar Kaduna), Bassey Akiba (jihar Cross River), Daulyop Fom (jihar Filato).
Sai kuma Erhiatake Ibori-Suenu (jihar Delta), wadda ‘yar tsohon gwamnan jihar ce, James Ibori, da ita ma ta fice daga PDP zuwa APC ɗin.
‘Yanmajalisar sun ce rikicin shugabanci da jam’iyyar tasu ke fama da shi ne dalilin da ya sa suka fice daga cikinta.
Ɗantakarar LP Peter Obi, shi ne ya zo na uku a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 da aka gudanar, abin da ya jawo wa jam’iyyar tagomashi karon farko cikin kusan shekara 20.