fidelitybank

‘Yan majalissa sun umarci jami’an tsaro su tare hanyoyin da ‘yan ta’adda ke tserewa

Date:

‘Yan majalisar dattawa sun umarci sojoji da sauran jami’an tsaron kasar da su sanya ido sosai tare da tare duk wasu hanyoyin da ‘yan ta’adda da barayin daji ke bi suna tserewa.

Jaridar DailyTrust ta rawaito cewa, ‘yan majalisar sun bayar da umarnin ne bayan gabatar da kuduri da mataimakin Gagarabadau, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi na jihar Neja ya yi, sakamakon sabbin hare-hare da satar mutane da ake yi a yankunan kananan hukumomin Mariga da Mashegu da Kontagora da kuma Borgu na jihar Neja.

Sanatan ya ce, “Sakamakon muggan hare-haren da sojoji da sauran jami’an tsaro ke kai wa ‘yan ta’adda da barayin daji da suka addabi yankunan gabashin jihar Sokoto da Zamfara, ‘yan ta’adda na ta tserewa suna shiga jihar Neja, ya kamata a tsara hare-haren da ake kai wa ‘yan ta’addar da kyau yadda ya kamata, ta yadda za a datse duk wata hanya da suke bi suna guduwa suna shiga sassan jihar Neja”.

Majalisar ta umarci hukumar bayar da agajin gaggawa NEMA da ta samar da kayan abinci da sauran muhimman abubuwa more rayuwa ga mutanen kauyukan da hare-haren ‘yan ta’addar ke shafa da kuma ‘yan gudun hijira a yankunan kananan hukumomin Mariga da Mashegu da Kontagora da kuma Borgu.

legit.ng.news.

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp