Wasu ‘yan majalisar dattawan Najeriya sun saya wa shugaban majalisar takardar takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki.
A yau Litinin ne ‘yan majalisar suka saya wa Ahmed Lawan takardar, inda wasu daga cikin ‘yan majalisar da suka hada da Sanata Bello Mandiya da Sanata Barau Jibrin da Sanata Yusuf A. Yusuf suka je sakatariyar jam’iyyar domin sayen fom din.
Sanata Ahmed Lawan shi ne, mai mukami mafi girm a majalisar dokoki ta tarayyar Najeriya, saboda haka ana kallon shiga takarar tasa a matsayin wani babban abu.
A baya dai wasu jiga-jigan jam’iyyar ta APC wadanda suka hada da tsohon gwamnan jihar Lagos, Bola Ahmed Tinubu da ministoci da wasu gwamnoni sun sayi takardar neman takarar, wadda jam’iyyar ke sayarwa a kan naira miliyan 100.