‘Yan majalisar dokokin jihar Edo sun fara shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu.
An karanta koken tsige mataimakin gwamnan ne a ranar Laraba a zaman majalisar.
Shugabar masu rinjaye, Charity Aiguobarueghian, wacce ta karanta karar tsige mataimakin gwamnan a zauren majalisar, ta ce mambobin 21 cikin 24 ne suka sanya hannu kan karar da suka shigar a kan mataimakin gwamnan.
Aiguobarueghian, ya ce an gabatar da karar ne a ranar 5 ga Maris, 2024, ya ce adadin mambobin da suka rattaba hannu kan takardar ya zarce kashi biyu bisa uku da ya tanada a sashe na 188 (2a) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya.
Ya ce an mika koken ne ga kakakin majalisar, Blessing Agbebaku.
Shugaban majalisar wanda ya amince da karbar koken ya ce an gabatar da karar ne bisa wasu dalilai guda biyu wadanda ba a bayyana su ba.
Sai dai majalisar ta baiwa mataimakin gwamnan wa’adin kwanaki bakwai ya amsa bukatar.
Shugaban majalisar ya umurci magatakardar majalisar, Yahaya Omogbai, da ya ba da sanarwar tsige Shaibu.
Watakila sanarwar tsige Shaibu ba ta rasa nasaba da rikicin sa da gwamnan jihar Godwin Obaseki wanda ya kai shi ga rashin nasara a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP da aka kammala a jihar.
Idan dai za a iya tunawa, Shaibu ya yi zargin yunkurin tsige shi daga mukaminsa, yana mai cewa burinsa na zama gwamna ne ke da alhakin shirin.
An zabe shi a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP a daidai lokacin zaben fidda gwani da aka gudanar a gidansa da ke birnin Benin, babban birnin jihar.
An kuma bayyana Asue Ighodalo a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP da ya gudana a filin wasa na Samuel Ogbemudia da ke Benin.