Wasu gungun ‘yan majalisa 35 da aka fi sani da masu neman sauyi, sun gabatar da wasu manyan sauye-sauye ga kundin tsarin mulkin kasar nan 1999, ciki har da gabatar da wa’adin mulki na shekara shida ga shugaban kasa da gwamnoni.
‘Yan majalisar dai na kuma ba da shawarar sauya kundin tsarin mulkin kasar nan, domin samar da mataimakan shugaban kasa biyu daga yankunan kudanci da arewacin kasar nan.
Wata babbar shawara da kungiyar ta zayyana ita ce, za a gudanar da zaben shugaban kasa tsakanin shiyyoyi shida da kuma gudanar da zabuka a rana guda.
Da suke yi wa manema labarai karin haske a ranar Litinin a zauren majalisar, ‘yan majalisar karkashin jagorancin Ikenga Ugochinyere, sun ce, sun gabatar da wasu sauye-sauye 50, inda suka ce an jera kudirorin guda shida a zauren majalisar.
Ugochinyere ya ce, kundin tsarin mulkin kasar nan ya nuna babban gibi da ya kamata a magance.