Jam’iyyar APC ta umurci majalisar dokokin jihar Ribas, karkashin jagorancin Rt. Hon. Martin Amaewhule da ya fara shirin tsige Gwamna Siminilayi Fubara nan take.
Shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC a jihar Ribas, Cif Tony Okocha, ne ya bayar da wannan umarni a taron manema labarai a Fatakwal, babban birnin jihar a ranar Talata.
‘Yawancin ‘yan majalisar dokokin jihar magoya bayan tsohon gwamnan jihar ne kuma ministan babban birnin tarayya na yanzu, Nyesom Wike.
Wike da Fubara na takun saka a tsakanin juna, tun bayan da ya mika ragamar mulkin jihar zuwa hannun Fubara.
Okocha ya ce, matakin da jam’iyyar ta dauka ya biyo bayan kalaman Fubara na cewa, tsoma bakin shugaba Bola Tinubu a rikicin siyasar da ya hana ruwa gudu a jihar, wanda hakan Fubara ke ganin bay a cikin ka’idar shari’a.
Okocha ya bayyana cewa, idan majalisar ta kasa fara shirin tsige Fubara, tabbas za ta yi amfani da sassan kundin tsarin mulki domin ladabtar da sun tsige shi.