fidelitybank

‘Yan majalisa 27 na Ribas da suka bar PDP sun rasa kujerar su – Edison

Date:

Shugaban ɗaya ɓangaren majalisar dokokin Rivers, Edison Ehie ya ayyana kujerun ƴan majalisa 27 da a baya-bayan nan suka fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC a matsayin na waɗanda babu kowa a kai.

An ɗauki wannan matakin ne da safiyar yau Laraba yayin zaman majalisar da Ehie ya jagoranta inda hakan ya zo daidai lokacin da ake rushe ginin majalisar dokokin.

Lamarin ya faru ne sakamakon sauya sheƙar da mambobin 27 suka yi ƙarƙashin jagorancin Martin Amaewhule, wanda shi ne shugaban ɗaya ɓangaren majalisar da ke goyon bayan tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike.

Majalisar dokokin jihar mai mambobi 32 ta tsunduma cikin rikicin shugabanci tun watan Oktoba inda ɓangarorin biyu da ke rikici da juna ke fafutukar ƙwace ikon majalisar.

Wata babbar kotu a Patakwal a baya-bayan nan kuma ta tabbatar da Ehie a matsayin halastaccen shugaban majalisar.

Kotun ta kuma hana magoya bayan Wike daga shiga harabar majalisar har sai an gama gyara majalisar da gwamnatin jihar ta ba da umarni.

www.nnn.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp