Da safiyar yau Asabar mataimakin magajin gari Mariupol ya faɗa wa BBC cewa Rasha ta ci gaba da yin luguden wuta a yankinsu duk da sanarwar tsagaita wuta da aka ce ta fara aiki da ƙarfe 7:00.
Sai dai ma’aikatar tsaron Rasha na bayyana wani abu daban da wannan.
Ta ce, ‘yan kishin ƙasa a Ukraine ne suka hana fararen hula ficewa daga garin, a cewar kamfanin labarai na Rasha, Ria.
Ma’aikatar ta ce, an kai wa dakarun Rasha hari bayan ta ayyana tsagaita wuta, domin fararen hula su fita daga yankin.